Labarai
NDLEA ta cafke miyagun kwayoyi na biliyoyin Naira
Hukumar yaki da sha da fataucin miyaguin kwayoyi ta Najeriya NDLEA, ta cafke kimanin kunshi 66 na wani nau’in tabar wiwi, kunshe kunshe a cikin koren ganyen shayi da aka shigo da su ta filin jirgi na Murtala Muhammed da ke Ikeja birnin Lagos.
Ccafke wadannan miyagun kwacen a ranar Alhamis, 5 ga Yuni, ya samo asali ne daga sahihan bayanan sirri da aka samu gabanin isowar kayan sashen jigilar kayayyaki na filin jirgin a ranar 11 ga Mayu.
Hukumar ta NDLEA ta sanya ido kan jigilar kayayyaki tare da ci gaba da sa ido a kai sama da makonni uku kafin ta gayyaci sauran masu ruwa da tsaki don yin aikin hadin gwiwa a ranar Alhamis din da ta gabata.
Wata sanarwa da Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na NDLEA, Femi Babafemi, ya sanya wa hannu a ranar Lahadi a Abuja, ta ce, an boye miyagun kwayoyin ne mai nauyin kilogiram 62 da digo 20 a cikin kwalayen ganyen shayin da aka yo safararsu daga kasar Thailand ta hanyar jirgin hadaddiyar daular Larabawa na Emirates.
You must be logged in to post a comment Login