Labarai
NDLEA ta cafke mutane 22 da ta ke zargi da sha da safarar kwayoyi a Kano

Hukumar hana sha da safarar miyagun ta kasa NDLEA ta kama mutane Ashirin da Biyu bisa zargin su da ta’ammali da dilancin miyagun kwayoyi a nan Kano.
Kwamandan hukumar na jihar Kano Abubakar Idris Ahmad, ne ya bayana hakan ta bakin mai magana da yawun hukumar Sadiq Muhammad mai garari, bayan Kai sumame guraren da ake dilancin miyagun kwayoyi a jiya alhamis.
Sadiq Muhammad mai gatari, ya kuma Kara da cewa wuraren da suka Kai sumamen sun hadar da filin Idi da Gwangwazo da sauran wasu wurare da suka yi kaurin suna.
Ya kara da cewa doka ta bai wa hukumar damar shiga duk wani gini ko gida da su ke zargin ana tu’ammali da miyagun kwayoyi don gudanar da bincike ko Kama wanda su ke zargi.
Hukumar ta NDLEA ta kuma bukaci mutane da su ci gaba da ba su bayanan sirri don daukar matakin da ya kamata ga masu safara dilanci ko tu’ammali da miyagun ta hanyar sanar da hukumar tare da ba da tabacin boye sirrin duk wanda ya bada bayani.
You must be logged in to post a comment Login