Connect with us

Labarai

NDLEA ta hada kai da Kwalejin Kano Polytechnic domin gyaran hali ga masu ta’ammali da miyagun kwayoyi

Published

on

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA, reshen jihar Kano, ta ce za ta haɗa gwiwa da Cibiyar Ci gaban Ƙwarewar Aiki ta Kwalejin fasaha wato Kano State Polytechnic wajen koyar da sana’o’i ga mutanen da aka yi wa gyaran halayya bayan shaye-shaye, da kuma waɗanda ke hannun hukumar.

 

Ta cikin wata sanarwa da ya aikewa manema labarai, mukaddashin jami’in hulda da jama’a na Kwalejin  Auwal Isma’il Bagwai  ta ce, ancimma matsayar ne yayin wata ganawa tsakanin jami’an NDLEA da shugabannin cibiyar a Kano State Polytechnic. 

 

Daraktan cibiyar, Comrade Abdullahi Ibrahim K/Nasarawa, ya yaba wa kwamandan NDLEA na Kano, CN Dahiru Yahaya Lawal, kan yadda yake ƙoƙarin ganin an rage matsalar shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi a jihar.

 

A nasa ɓangaren, jami’in NDLEA mai kula da yaƙi da hana shaye-shaye, ACN Mu’awiya Alkali, wanda ya wakilci kwamandan jihar, ya ce shirin zai taimaka wajen bai wa waɗanda suka daina shaye-shaye damar dogaro da kansu da kuma samun halal ɗin sana’ar yi. Ya ce hakan zai rage yiwuwar komawar su cikin shaye-shaye ko fataucin miyagun ƙwayoyi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!