Labarai
Atiku ya bukaci Gwamnatin Tinubu ta yi bayani kan bashin da ta karba na Biliyan 5

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kana dan takakar shugaban kasa a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bukaci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bayyana cikakkun bayanai kan yadda za a yi amfani da bashin dala biliyan 5 da Najeriya ta samu daga bankin Abu Dhabi.
Atiku ya soki kalaman Ministan Kuɗi, Taiwo Oyedele, na cewa gwamnati ba za ta fitar da cikakken bayani kan yadda za a kashe kuɗin ba. Ya ce ’yan Najeriya da kuma al’ummomin da za su zo nan gaba ne za su ɗauki nauyin biyan bashin, don haka gwamnati na da alhakin yin cikakken bayani kan yadda za a yi amfani da shi.
Ya kuma yi zargin cewa yawan basussukan Najeriya ya ƙaru sosai tun bayan hawan Tinubu kan mulki, yana mai cewa duk da karɓar sabbin basussuka, talauci da rashin tsaro sun ƙaru.
Atiku ya bukaci ’yan Najeriya su riƙa neman gwamnati ta ba da cikakken bayani kan yadda ake amfani da kuɗin aro, domin gujewa abin da ya kira rashin gaskiya da kuma barazana ga makomar tattalin arzikin ƙasa.
You must be logged in to post a comment Login