Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NDLEA ta kama mutane sama da 84 yayin samame a Kano

Published

on

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA shiyyar Kano, ta ce, ta samu nasarar kama sama da mutane 84 a wani samame da ta kai wurin shakatawa na Bubble Club a cikin birnin na Kano.

Hukumar, ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar ASN Sadik Muhammad Maigatari ya fitar ranar Talata.

ASN Sadik ya ce, sun samu korafe-korafe daga mazauna yankin cewa suna zargin an mayar da wurin na shaye-shayen miyagun kwayoyi wanda hakan ya sa kwamandan hukumar Abubakar Idris, ya fara tura jami’an hukumar na farin kaya domin tabbatar da zargin, kuma daga bisani ya bada umarnin tura dakarun hukumar cikin shirin ko-ta-kwana tare da killace wurin baki daya.

Ta cikin sanarwar ASN Sadik ya ce, bayan kai samamen hukumar ta samu nasarar kama maza 55 da kuma mata 30 a yayin da wasu suka yi kokarin haura katanga wasu kuma suka yi yunkurin buya a cikin na’urar sanyaya ruwan sha, amma daga bisani jami’an hukumar sun cafke su.

Sanarwar ta kara da cewa hukumar NDLEA ba za ta saurara ba wajen ganin ta kawo karshen duk wasu dilolin kwayoyi da kuma masu shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar Kano.

 

Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!