Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun dawo da martabar Masarautu ne don gina sabbin Birane- Ganduje

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya ce, gwamnatinsa ta dawo da martabar sababbin Masarautu ne domin gina sabbin Birane a jihar.

Gwamna Ganduje ya bayana hakan lokacin da yake kaddamar da babban asibitin Masarautar Karaye da yammacin ranar Talatar makon nan, bayan bude ayyukan titi a karamar hukumar Rano da kuma Karaye.

Haka kuma Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kuma bukaci mazauna Masarautar ta Karaye da kewayenta da su yi amfani da asibitin yadda ya dace.

Gwamna Ganduje, ya kuma ziyarci wurin da ake gudanar da aikin samar da wutar lantarki mai zaman kanta ta jihar Kano a Dam din Challawa da ke yankin karamar hukumar Kumbotso.

 

Rahoton: Abba Isah Muhammad

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!