Connect with us

Labarai

NELFUND ya musanta rahoton ƙara kuɗin alawus din ɗalibai

Published

on

Asusun bayar da lamunin kudin karatu na kasa NELFUND, ya musanta rahotannin da ke cewa an ƙara kuɗin alawus na ɗalibai zuwa naira dubu ashirin da biyar.

A cewarsa, adadin kuɗin wata-wata yana nan a kan naira dubu ashirin, kamar yadda aka amince tun da fari.

A cikin wata sanarwa da daraktan sadarwa na hukumar, Oseyemi Oluwatuyi, ya fitar, an buƙaci ɗalibai da su yi watsi da duk wani bayani da ba daga hukumomin NELFUND ya fito ba. 

Tun bayan fara shirin a shekarar 2024, NELFUND ta raba sama da naira biliyan dari biyu da shida ga ɗalibai sama da miliyan ɗaya da dubu ɗari shida a manyan makarantu. An kuma tsara cewa za a fara biyan bashin ne bayan kammala karatu da samun aiki, domin rage wa ɗalibai nauyin biyan a yayin da suke karatu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!