Labarai
NEMA da IOM sun karɓi yan Najeriya 145 da aka dawo daga Libya

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA tare da haɗin gwiwar Ofishin Kula da Shige da Fice na Ƙasa da Ƙasa IOM sun karɓi ‘yan Kasar nan 145 da suka dawo daga birnin Benghazi na kasar Libya, a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Ikeja.
Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Ofishin Kula Ayyuka hukumar na jihar Legas Mohammed Olatunde, ya sanya wa hannu, aka rabawa manema labarai.
Cikin mutanan da aka dawo dasu sun hadar da manya 122 wanda suka kunshi maza 46 da kuma mata 76 yayin da yara suka kasance su 29 maza 13 mata 16.
You must be logged in to post a comment Login