Labarai
NEMA ta tabbatar da mutuwar jami’an gwamnati 2 a hatsarin Lagos
Wani Jirgin kasa a Jihar Lagos da ya yi taho mu gama da wata motar Bas a kan hanyarsa da ke Ikeja babban birnin jihar.
Rahotonni sun bayyana cewa, ana fargabar rasuwar ma’aikatan gwamnatin jihar biyu yayin da wasu kuma da dama suka jikkata sakamakon taho mu gama din da jirgin kasan ya yi da motar da safiyar yau Alhamis.
Motar na dauke da wasu ma’aikatan gwamnati ne, wandada suke kan hanyarsa ta zuwa wurin aiki inda a kokarin da motar ta yi na tsallaka layin dogon ne aka samu afkuwar iftila’in dai-dai lokacin da jirgin ke wucewa ta wurin.
Mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta NIjeriya NEMA Ibrahim Farinloye, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, an gano gawarwakin ma’aikatan gwamnati mata biyu, an kuma kwashe wadanda suka jikkata da dama.
You must be logged in to post a comment Login