Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

DSS ta bankado yunkuri tayar da tarzoma bayan zabe

Published

on

  • DSS ta gano wani yunkurin tayar da tarzoma yayin gudanar da zabe a Nijeriya.
  • Wasu mutane sun yi shirin tayar da rikici bayan kammala zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha.
  • Shugaban DSS Peter Afunanya ya ce ire-iren matsalolin babbar matsala ce ga damukradiya.

Hukumar tsaro ta DSS a Nijeriya ta gano wani yunkuri na tayar da tarzoma yayin da ake kara tunkarar zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi.

A cewar hukumar ta DSS, ‘wasu mutane da ba ta kai ga bayyana sunan su ba, na shirin ta da rikici bayan kammala zaben gwamnonin jihohi, da aka shirya yi a ranar Asabar 11 ga wata, daga bisani aka mayar da shi ranar 18 ga watan Maris din bana.

A cikin sakonnin da jami’in hulda da jama’a na hukumar Peter Afunanya ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce kulle-kulle da ‘yan siyasa ke yi domin cimma burikansu na ‘kashin kai/

Haka ya kara da cewa yin hakan zai haifar da babbar matsala ga damukaradiyyar Nijeriya.

A  don haka ya bayyana cewa ‘a shirye hukumar take wajen dakile ire-ien matsalolin nan a fadin kasar nan baki daya’.

 

Rahoton: Ahmad Kabo Idris

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!