Labarai
NEMA zata maye gurbin motocin da rikicin shi’a ya lalata
NEMA zata maye gurbin motocin da rikicin shi’a ya lalata
Hukumar agajin gaggawa ta kasa NEMA ta ce, zata kashe Naira milliyon dari biyu don sayen motocin daukan marasa lafiya da nufin maye gurbin wadandan suka kone a rikicin da ya auku tsakanin jami’an kasar nan da kungiyar mabiya shia a watan Yulin daya gabata.
Baban daraktan hukumar Mustapha Maihaja ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai.
Maihaja ya kuma ce, kawo yanzu shirye-shirye sun yi nisa na fara aiwatar sayen motocin don gudanar ayyukan su yadda ya kamata, ba tare bata lokaci ba.
Yana mai cewa, tuni gwamnatin tarraya ta amince da sayen motocin daukan marasa lafiya.