Connect with us

Labaran Kano

Zamu maye gurbin ma’aikatan da suka yi ritaya na Asibitin Murtala- Ganduje

Published

on

Gwamnati jihar Kano tace nan da makwanni biyu zata maye gurbin ma’aikatan lafiya dake Asibitin Murtala Muhammad wadanda suka yi ritaya da kuma wadanda suka mutu domin cigaba da bunkasa harkokin Lafiya a fadin Jihar Kano.

Shugabar Ma’aikata ta jihar Kano Hajiya Binta Lawan Ahmad ce ta bayyana hakan lokacin data kai wata ziyarar bazata tare da tawagar ma’aikatan Hukumar kula da ayyukan gwamnati zuwa Asibitin kwararru na Murtala domin ganin yadda ayyuka ke gudana.

Hajiya Binta Lawan Ahmad ta kuma yabawa shugaban Asibitin Murtala Muhammad Dr, Usaini Muhammad bisa yadda ta iske yana duba marasa lafiya da sanyi safiya kuma ta samu Asibitin cikin yanayi mai tsafta.

Da yake jawabi lokacin ziyarar Shugaban Asibitin Murtala Muhammad Dr Usaini Muhammad ya yabawa tawagar shugabar ma’aikatan tare da mika bukatar neman maye gurbin Ma’aikatan Asibitin da sukayi ritaya domin samarda ingantacciyar lafiya a Kano.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,159 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!