Kiwon Lafiya
Nigeria da kasar Morocco sun amince kan yarjejeniyar safarar iskar gas
Nigeria da kasar Morocco sun amince da sanya hannu domin tabbatar da yarjejeniyar kafa bututun safarar iskar gas zuwa yankin Arewacin Africa zuwa gabar kogin Atlantic da suka yi a baya.
Kafar sadarwa ta kasar morocco ta ruwaito cewar manyan jami’an gwamnatin kasashen biyu ne suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya a birnin Rabat na kasar Morocco lokacin da suke karin bayani kan yadda za a inganta yarjejeniyar da aka cimma tun a shekarar 2016.
Kasashen biyu sun amince da lalubo hanyar da za yi kari kan bututun iskar gas da ya tashi daga kudancin kasar nan da ya ketare ta kasar Benin, yabi ta Togo ya kuma tuke a kasar Ghana tun a shekarar 2010.
Wannan batu dai na samar da bututun iskar gas daga Najeriya zuwa yankin Arewacin Africa batu ne da aka dade ana bukatar sa tun wani lokaci mai tsaho.
Ko a baya kasar Algeria ta tattauna batun da kasar nan tun a shekarar 2002 kan samar da bututun iskar gas din, sai dai kasar ta Algeria ta gaza daukar nauyin gudanar da aikin.