Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Nijar: A janye dokar hana hawa Babur a Tillaberi

Published

on

Hukumomi a jamhuriyar Nijar sun janye dokar hana hawa Babur a jihar Tillaberi, mai fama da hare-haren ƴan ta’adda.

Shugaban majalisar dokokin ƙasar Alhaji Saini Ommarou ne ya sanar da hakan yayin ziyarar da ya kai jihar ta Tillaberi.

Hakan kuma ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da jama’ar jihar suka riƙa yi, ciki har da ƴan majalisun jihar.

Janye dokar zai fara aiki ne daga ranar Laraba mai zuwa.

Al’umma da dama ne dai a jihar suka riƙa nuna farin cikinsu bayan da Gwamnati ta amince da wannan buƙata da suka nema.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!