Labarai
Nijar: gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki na kwana 3 sakamakon hare-haren mayaka
Nijar: gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki na kwana 3 sakamakon hare-haren mayaka
Gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makoki na tsawon kwana uku da za a fara yau Talata, sakamakon wasu hare-hare da mayaka da ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kai kan wasu kauyuka uku a jihar ranar Lahadi inda suka kashe mutane 137.
Hukumomin Nijar din sun sanar da makokin ne, tare da tabbatar da yawan mutanen da maharan suka hallaka a jerin hare-haren da suka kai a kauyukan da ke kan iyaka da kasar Mali da Burkin Faso da yammacin Lahadi.
Kafin sanarwar da hukumomin a Nijar suka fitar an yi ta bayar da alkaluma na yawan wadanda ‘yan bindigar suka hallaka, zuwa mutum 40, amma kuma da wannan sanarwar ta hukuma, ta tabbatar cewa, mutanen sun wuce haka nesa ba kusa ba.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi dauki ba dadi tsakanin jami’an tsaro da maharan, wadanda daga baya suka gudu zuwa yankin iyakar Mali.
Nijar dai na fuskantar munanan hare-haren da ba ta saba gani ba a baya bayan nan, daga masu ikirarin jihadi, da kan kai farmaki a kan kauyuka ta hanyar amfani da Babura da motocin a-kori-kura galibi a yankuna na kan iyaka.
You must be logged in to post a comment Login