Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro: harin yan ta’adda ya sanya mazauna Damasak tserewa zuwa Nijar

Published

on

Ya zuwa yanzu, akalla mutane dubu dari ne suka tsere daga garin Damasak na jihar Borno zuwa Jamhuriyar Nijar mai makwabtaka da su a Larabar nan,  sakamakon yawaitar hare-haren mayakan Boko Haram.

Hukumomin gwamnati sun ce aƙalla mutane 10 aka kashe a Larabar nan, yayin da wasu da dama suka ji rauni, kana wasu dubbai suka bazama cikin dazuka.

A cewar su, ya zuwa yanzu, akalla mutane dubu dari ne suka tsere daga garin Damasak na jihar Borno zuwa Jamhuriyar Nijar mai makwabtaka da su a Larabar sakamakon yawaitar hare-haren mayakan Boko Haram.

An kuma gano cewa daruruwan gidaje na farar hula, da shagunansu da gine-ginen gwamnati gami da hedkwatar rundunar ‘yan sanda sun kone kurmus sakamakon cinna musu wuta da maharan suka yi.

Harin na Laraba a Damasak, an sanya shi a jerin hare-hare mafi muni, wanda kuma shi ne na karo na shida a cikin makonni biyu da suka gabata.

Sai dai har kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance da ta fito kan matsayin garin, wanda ya zuwa yanzu kimanin shekaru 11 kenan yankin na fama da hare-haren ‘yan ta’addan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!