An Tashi Lafiya
Nijar ta karɓi bashin miliyan dubu ɗari biyu da ashirin na Cefa, domin yaƙi da matsalar yunwa da kuma inganta rayuwar al’umma
Jamhuriyar Nijar ta samu rancen kuɗi daga Bankin Duniya sama da miliyan dubu dari biyu da ashirin na Cefa, dai-dai da dalar amurka miliyan dari huɗu, domin tunkarar matsalar yinwa da inganta rayuwar al’ummar kasar.
Tuni dai wasu kungiyoyin manoma da na raya ayyukan karkara suka fara tofa albarkacin bakinsu akan samun bashin.
Shugaban ƙungiyar mutanan karkara Malam Abdu Gajango ya bayyana farin cikin sa, game da wannan ƙudiri, ya kuma ƙara da cewa, ya kamata Gwamnati ta mai da hankali a wuraren da suka fi buƙata, tare da mai da hankali akan su kansu makiyaya ta kuma guji yin “rabon ɗan kishiya.”
Ayyukan da Gwamnatin zata gudanar sun haɗa da, gina magudanan ruwa, ceto gandun daji, da kuma samar da ingantaccen ruwan sha a yankunan karkara, sai kuma samarwa da makiyaya mashayar dabbobi. Ana kuma sarai aƙalla mutane miliyan uku ne zasu ci gajiyar waɗannan ayyukan.
You must be logged in to post a comment Login