Connect with us

Labarai

Buhari zai sake nazartar kasafin kudi sakamakon bullar cutar Corona

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce bullar cutar Corona da kuma faduwar farashin gangar danyan mai, ya sanya dole ta sake nazartar kasafin kudin wannan shekara.

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmed ce ta bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa, bayan kammala taron majalisar zartaswa ta kasa.

Ta ce, bullar cutar ta sanya wajibi gwamnati ta sake nazartar kasafin kudin saboda ya zo mata a bazata.

Haka zalika ministar ta kuma ce, farashin gangar danyan mai ya fadi a kasuwannin duniya, inda a yanzu ake sayarwa akan dala hamsin da biyu.

Anyi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen matsalar tsaro

Buhari zai yi titi daga Sokoto zuwa Nijar

Bashin da ake bin Najeriya ya ninka kasafin kudin badi-Akibu Hamisu

wanda hakan ya yi kasa da yadda aka tsara kasafin kudin kasar nan akan dala hamsin da bakwai.

Sai dai ta ce, an samu ci gaba ta bangaren hakar mai domin yanzu kasar nan tana iya fitar da ganga miliyan biyu da dubu dari daya a duk rana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,812 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!