Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Wasu cikin muhimman al’amuran ilimi da suka faru a 2022

Published

on

  • A cikin shekarar ne gwamnatin Kano ta amince da sauya wa jami’ar KUST suna zuwa jami’ar Aliko Dangote.

 

  • A shekarar ne tsarin bayar da ilimi kyauta ya yi tasiri a nahiyar Turai

 

Shekarar 2022, shekara ce da ta zama kyakkyawar makoma ga tsarin ilimi a kasar Amurka, bayan da fannin ya samu tasgaro na shekaru biyu sakamakon annobar cutar Corona da ta mamaye duniya.

Domin kuwa kasashen sun samar da sabbin matsuganai ga dalibai da kuma fito da sabbin tsare-tsaren koyarwa ta kafar Intanet, baya ga sabbin dabarun inganta koyarwar.

A nahiyar Turai kuwa tsarin nan na ba da ilimi kyauta ne ya yi tasiri a bangaren inganta harkokin ilimi, domin kuwa kasashe sama da 37 ne a nahiyar ke amfana da tsarin, wajen bai wa dalibai ilimi da horo.

Fannin ilimi a nahiyar Afirka musamman yankin Yammaci da Tsakiyar Afirka, an samu karuwar yawan makarantun da aka rufe saboda rashin tsaro a cikin shekarar.

Domin kuwa ya zuwa karshen shekarar an rufe makarantu sama da dubu goma sha biyu da dari hudu a kasashe takwas na yankin, sakamakon hare-haren kungiyoyin ‘yan ta’adda, ko kuma matsalar karancin malamai, ko kuma saboda tsoron da iyaye ke yi na tura ‘ya’yansu makaranta don kada a yi garkuwa da su.

Karuwar rikice-rikice sun tsananta, har ma sun yi mummunan tasiri wajen rufe makarantu 12, daga watan Yunin da ya gabata a kasashen Burkina Faso, Kamaru, Chadi, Dimokradiyyar Congo, Mali, Nijar, da nan Najeriya.

A dai nan gida Najeriya, inda rahoton asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya nuna cewa sama da yara miliyan 18 da dubu dari biyar ne ba sa zuwa makaranta, adadin da ya karu idan aka kwatanta da na bara da yawan yara miliyan 10 da dubu dari biyar.

To sai dai a shekarar ne gwamnatin tarayya ta alkawarta kara kudin da ta ke kashewa a bangaren ilimi daga kashi 50 zuwa 100 a cikin shekaru biyu masu zuwa, da kuma kashi 100 cikin 100 nan da shekara ta 2025.

Ko a cikin kasafin kudin bana da yawansa ya kai Naira tiriliyan 17, gwamnatin tarayya ta ware kashi 7.2 ga bangaren ilimi, kuma hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kashi 35 cikin 100 na yaran da ke zuwa Furamare ba sa samun damar tsallakawa zuwa sakandare, ta yadda suke yanke kauna da samun kyakkyawar makoma.

Bincike ya nuna cewa babbar matsalar da ke janyo rashin zuwan yara makaranta bai wuce rashin samar da makarantu a yankunansu ba, musamman ga mazauna karkara, baya ga matsalar tsaro da yawan faduwa a jarrabawa, wanda hakan ke cire wa yaran da iyayensu sha’awar yin karatun.

Sai dai a iya cewa matsalolin rashin tsaro da fannin ilimi ya fuskanta a bara an samu saukinsa a bana, sai dai kuma dogon yajin aikin watanni tara da kungiyar malaman jami’o’in kasar nan ta yi sakamakon rashin biya mata bukatunta daga gwamnati ya gurgunta bangaren, musamman ga jami’o’i.

An dai kai ruwa rana kafin daga bisani kungiyar ASUU ta sanar da janye yajin aikin na watanni 9, wanda ta fara tun a watan Fabrairu, abinda ya jefa dalibai har ma da malaman cikin mawuyacin hali, musamman yadda gwamnati ta ce ba za ta rinka biyansu albashi ba.

Daga nan ne ma gwamnatin ta kirkiro wata sabuwar kungiya mai taken CONUA da nufin ta maye gurbin ASUU, wanda daga nan ne kuma jami’o’in suka shirya wata zanga-zanga da yajin aikin wuni guda, don nuna kin amincewarsu da matakin gwamnatin.

Haka su ma Kwalejojin ilimi da na kimiyya da fasaha duk sun yi yajin aiki a shekarar, ko da yake tasirinsa bai yi muni ba kamar na ASUU.

Idan muka dawo nan Kano kuwa, masu sharhi kan al’amuran ilimi sun alakanta faduwar jarrabawar kwalafayin da rashin fitar da sakamakon jarrabawar daliban Arabiyya ta NBIS da ƙaruwar talauci da kuma rashin tasirin tsarin ba da ilimi kyauta kuma dole, a matsayin abinda ya haifar da karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta.

Ko a kasafin kudin shekarar nan mai karewa gwamnatin Kano ta alkawarta tabbatar da tsarin ba da ilimi kyauta kuma dole, ta hanyar ware masa kaso mai tsoka, haka abin yake a kasafin badi ma da gwamnatin ta gabatar, har ma ta ce kasafin zai fi mayar da hankali wajen bunkasa harkokin ilimi.

A shekarar ne dai kuma a wani mataki na farfaɗo da harkokin ilimi, majalisar wakilai ta amince da tsarin koyar da dalibai da harshen uwa, kuma wannan kudiri yana cikin muhimman batutuwa da masana suka ce za a iya cin gajiyarsa wajen farfaɗo da harkokin ilimi.

A cikin shekarar ne gwamnatin Kano ta amince da sauyawa jami’ar kimiyya da fasaha ta garin Wudil suna zuwa jami’ar Aliko Dangote.

 

Rahoton: Aisha Aliyu Getso

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!