Labarai
NiMet ta gargadi masu fama da Asma da cutukan numfashi da su yi taka-tsantsan

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet, ta shawarci mutanen da ke fama da lalurar Asma da sauran matsalolin numfashi da su yi taka-tsantsan da yanayin da ake ciki a yanzu da kuma hasashen fuskantar karin yanayin hazo.
Hukumar, ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta fitar da yammacin ranar Lahadi a shalkwatar ta da ke birnin tarayya Abuja.
A cewar sanarwar akwai bukatar jama’a su dauki matakan kariya domin kare lafiyarsu.
You must be logged in to post a comment Login