Labarai
NiMet ta yi hasashen yin Hazo da ruwan sama a wasu sassan Najeriya

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya NiMet ta yi hasashen cewa za’a samu yanayin Hazo da kuma ruwan sama a wasu sassan Najeriya nan daga yau Litinin zuwa Laraba.
Hakan na cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta a X.
Cikin jihohin da hukumar ta yi hasashen za a iya fskantar wannan yanayi hadar da Borno da Zamfara da Yobe da Jigawa da Katsina da Kaduna sai kuma Kano
Cikin wani rahoton da hukumar ta fitar ranar Lahadi ta buƙaci al umma su zama cikin shiri domin tunkarar waɗannan yanayi.
Haka ma hukumar ta ce akwai hasashen samun ruwan sama haɗe da tsawa a wasu yankunan jihohin Taraba da Adamawa.
Hukumar ta kuma yi hasashen samun rana a wasu jihohin arewa ta tsakiyar ƙasar, da kuma yiwuwar samun ruwan sama a jihohin Nasarawa da Kogi da Birnin Tarayya Abuja.
You must be logged in to post a comment Login