Labarai
NLC da TUC na shirin yin zanga-zangar goyon baya ga Ma’aikatan Abuja

Gamayyar kungiyoyin ƙwadagon Najeriya na NLC da TUC, sun bayyana shirin su na gudanar da zanga-zangar goyon baya a gobe Talata 3 ga Fabrairu domin tallafa wa Kwamitin hadin kan kungiyoyin Ma’aikata na birnin tarayya Abuja.
Zanga-zangar ta na goyon bayan ma’aikatan na Abuja da suka shiga yajin aikin sai baba ta gani tun 19 ga Janairu sakamakon batun biyan albashi da walwalar ma’aikatan.
Ta cikin wata Sanarwarwa mai dauke da da hannun Mr. Benson Upah, Sakatare Janar na NLC, da Mr. Nuhu Toro, Sakatare Janar na TUC, a Abuja.
An umurci dukkan rassan kungiyoyin da kwamitocin jihohi da su hada kai domin gudanar da zanga-zangar, har sai an samu biyan bukata.
You must be logged in to post a comment Login