Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NLC: Za muyi kokari wajen ganin ba a sake samun sa-in-sa ba tsakaninmu da gwamnati

Published

on

Kungiyar Kwadago ta kasa NLC ta ce za ta ci gaba da bibiyar gwamnatin Jihar Kano domin ganin ta mayarwa ma’aikata kudin da ta zaftare musu na albashin watan Maris.

Shugaban kungiyar reshen jihar Kano Kwamared Kabiru Ado Minjibir ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin “Barka da Hantsi” na nan Freedom Radio.

Shirin dai ya mayar da hankali ne kan yadda kungiyar ta yi yunkurin tafiya yajin aiki sakamakon zaftarewa ma’aikata albashi da gwamnatin jihar Kano ta yi.

Kabiru Ado Minjibir ya kuma ce kungiyar za ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin ba a sake samun wata sa-in-sa tsakaninta da gwamnati ba.

“Za mu dauki mataki kan wasu baragurbin jami’an gwamnati da ke dibarwa ma’aikata kudi da sunan ba shi,” a cewar Kwamared Minjibir.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!