Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za mu dauki tsattsauran mataki kan masu rufe gidajen mai don tsawwala farashi a Kano – Muhyi

Published

on

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta yi gargadin daukar tsattsauran mataki kan masu gidajen sayar da man fetur da ke tsawwalawa al’umma farashi.

Shugaban hukumar Barista Muhiyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai, sakamakon yadda aka fara fuskantar karancin man a Jihar Kano, a dalilin rufewar da wasu gidajen man suka yi.

Ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da zagayawa cikin kasuwanni don binciko masu kara kudin kayan masarufi.

Muhuyi Magaji Rimin Gado ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwar da su sausautawa jama’a a daidai wannan lokaci na fara ibadar watan azumin Ramadan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!