Kiwon Lafiya
NNPC:Karancin mai da aka samu a kwanakin baya son rai wasu dillalai ne
Gwamnatin tarayya ta ce matsalar karancin man fetur da aka yi fama da shi a kasar nan abaya-bayan nan saboda son rai na wasu Dillalan man fetur, ya kusan zamowa tarihi sakamakon irin kyawawan matakai da kamfanin mai na kasa NNPC ke dauka.
Shugaban kamfanin mai na kasa NNPC Mai Kanti Baru ne ya bayyana hakan, lokacin da yake ganawa da manema labarai a gefen taron shekara-shekara da kungiyar masana harkokin ma’adinai da Albarkatun karkashin kasa ta kasa su ke gudanarwa.
Ya ce tuni aka yi nisa wajen hakar man fetur a wasu yankuna na Arewacin kasar nan wadanda suka hada da: tabkunan Chadi da Gongola da kuma yankunan fadamun Benue.
Da yake gabatar da jawabi gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jiha Alhaji Usman Alhaji, ya ce nan ba da dadewa ba gwamnatin Kano za ta yi hadin gwiwa da kwararru domin gano yankunan da ke da ma’adinai a kananan hukumomin jihar 44.
Wakilin mu na gidan gwamnatin Kano Aminu Halilu Tudun-wada ya ruwaito cewa, dukkan-nin mutane 44 da aka horas da su a sana’oin sarrafa duwatsu masu daraja wadanda gwamnatin Kano ta dauki nauyin su, sun karbi takardar shaidar kammala karatun su da kuma wasu kayayyakin aiki na hakar ma’adinai, yayin da kuma taron zai ci gaba da gudana.