Connect with us

Labaran Kano

NNPP ta zargi gwamnatin Kano da muzgunawa mambobinta

Published

on

Jam’iyyar  NNPP reshen Jihar Kano  ta zargi gwamnatin jihar da yi wa mambobinta muzgunawa da tsangwama ta siyasa.

A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar a jihar, Ibrahim Karaye, ya fitar a hedikwatar jam’iyyar da ke Kano, ya bayyana matakin a matsayin wanda ya saba da dimokuradiyya tare da kira ga gwamnati ta daina abin da ya kira gallazawa mambobin jam’iyyar.

 

Karaye ya ce, “Wannan tsangwama ta siyasa da ake yi wa mambobinmu ba ta dace ba ce kuma cin zarafi ne ga ikon dimokuradiyya. Muna kira ga gwamnatin Kano ta dakatar da duk wani mataki na tsoratar da ‘yan kasa da ke da ‘yancin shiga kowace jam’iyya da suke so.”

Ya kuma yi zargin cewa gwamnatin da ta hau mulki a karkashin NNPP kafin ta raba gari da jam’iyyar, na daukar matakai kan wasu daga cikin mambobinta.

 

 

Jam’iyyar ta kuma yi zargin cewa ana matsa wa tsoffin jami’an gwamnati su mayar da motocin da aka ba su yayin da suke kan mukami, tana mai cewa motocin na daga cikin hakkokinsu a lokacin da suke aiki.

 

NNPP ta jaddada cewa ya kamata a gudanar da harkokin siyasa cikin mutunta juna, tana mai tunatar da cewa mukaman siyasa ba na dindindin ba ne. Haka kuma ta bukaci gwamnati ta mutunta ‘yancin haduwa da kungiya kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!