Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Noma: Mun rabawa manoma sama da biliyan dari 3 na tallafi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatin sa ta rabawa manoma Miliyan 1 da dubu dari 6 kudi sama da naira Bilyan dari 300 na tallafin noma.

Shugaban Buhari ya ce tallafin wani mataki ne na inganta harkar noma a fadin kasar nan.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin da ya kaddamar da taron bankunan kasuwanci na shekara-shekara karo na 14.

Muhammadu Buhari, ya kara da cewa babban bakin kasa na CBN, ya rabawa kananan manoma sama da miliyan uku naira biliyan dari 300, a bangarori noma daban-daban sama da 21.

Shugaban yace daga cikin wdana da suka samu tallafin, sun hada da manoma masara shinkafa rogo da kuma masu kiwon kifi da kaji.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!