Labarai
Noman Dabbino na da ribar gaske -Sarkin Pindiga
Sarkin Pindiga dake karamar hukumar Akko a jihar Gombe,, mai martaba Alhaji Muhammad Seyoji Ahmad , ya bukaci Gwamnatin tarayya da na jihohi da su samar da tsari mai dorewa akan Noman Dabino da Sarrafa shi tare da kasuwancin sa a fadin kasar nan.
Sarkin ya bayyana haka ne a yau lokacin da ya kai ziyara ,ta musamman ma’aikatar aiyyukan Gona ta jihar Kano, a cikin tsare -tsare gabatar da shirin ga gwamnatin jihar Kano , a bangaren daya kuma da kaddamar da Jagorancin Manoman Dabino na jiha.
Sarkin na Pindiga Muhammad Seyoji Ahmad, yace akwai riba mai yawa a Noman na Dabino ciki har da samar da aiyyukan yi ga matasan da basu da aiyyuka a Karkara , ba wai laruwa zuwa ga Mai na Fetur da sauran Ma’adinai a matsayin hanyoyin samar wa da kasar nan kudaden shiga.
A nasa jawabin, mataimakin gwamnan jihar Kano Nasiru Yusuf Gawuna, wanda mai baiwa gwama shawara na musamman akan harkokin Noma Hafiz Muhammad , ya wakilta ya ce shirin ana sa ran Noma Dabino Hekta (Hectre ) dubu Talatin a fadin jiha , da zarar an fara shirin karkashin tallafin banki kasa CBN da Bankin Duniya.
Wakilin mu Aminu Halilu Tudunwada ,ya ruwaito mana Sarkin na Pindiga tun da fari ya kai ziyara ga Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero , tare da gabatar masa da shirin wanda ake sa ran mutum dubu dari da Ashirin ne zasu samu aiyyukan yi da an kaddamar da shi a jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login