Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Za a sabinta tsarin gine-gine a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, zata samar da sabbin tsare-tsaren gine-gine da sabbin taswira a kan tsarin da aka shirya ginin jihar Kano tun Asali , wato Master Plan , sakamakon karan tsaye da ake wa tsarin da ya haifar da Cunkoso da lalacewar tsarin gine-gine.

Shugaban kwamitin ƙasa da safiyo na majalisar fokoki ta jihar Kano, kuma ɗan majalisar mai wakiltar ƙaramar hukumar Bunkure Muhammad Uba Gurjiya Mai Shanu, ne ya bayyana haka ta cikin shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio.

Muhammad Uba Gurjiya , ya ƙara da cewa duba da yadda al’umma ke ƙara yawa da yawaitar gine-gine wanda ba sa kan tsarin asali, ya sanya aka fito da sabon tsarin da zai zama wajibi kowa ya bi, musamman ma masu awon Igiya.

Ɗan Majalisar, yace daga ɓangaren kasuwanni da tsarin da suke dashi na ganin cewar an rage cunkoson su ta hanyar bin tsarin da ya dace tare da komawa sabbin kasuwannin da aka tsara.

Wakiliyar mu Maryam Ali Abdullahi da ta bibiyi shirin ta ruwaito cewa, sabon tsarin ya ƙunshi shigo da dukkan masu riƙe da madafun iko, kama daga ƴan siyasa, zuwa sarakuna da masu ruwa da tsaki akan harkar ƙasa da safiyo, don samar da kyakkyawan tsari irin na manyan biranen da suka yi shuhura.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!