Connect with us

Labarai

Northern Media Forum ta yi alhinin rashin Isah Funtua

Published

on

 Kungiyar shugabannin kafafan yada labarai ta Arewa wato Northern Media Forum, ta bayyana rasuwar marigayi Alhaji Isama’ila Isa Funtuwa a matsayin babban rashi a kasar nan mussaman ma a bangaren aikin jarida.

A cewar kungiyar, marigayi Isa Funtuwa wani jigo ne a aikin jarida a kasa da ma kasashen waje.

Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da shugaban kungiyar Dan Agbese ya sanya wa hannu, sanarwar ta ce kafin rasuwar sa marigayi Isama’ila Isa Funtua na uban cibiyar nazari kan aikin jarida ta kasa da kasa kazalika uba  ne a kungiyar masu gidajen jaridu ta kasa wanda ba za’a taba mantawa da shi ba kan irin gudunmawar da ya bayar wajen bunkasa wannan bangare.

Yayin da kungiyar ta Northern Media Forum ke alhinin rasuwar marigayin ta aike da ta’azziyar ta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da al’ummar jihar Katsina da ma iyalan marigayin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!