Kiwon Lafiya
NPC: ta ce galibin tsawon ran ‘yan Najeriya baya wuce shekaru 52 a duniya
Hukumar kidaya ta kasa NPC ta ce a halin yanzu galiban tsayin ran da ‘yan Najeriya suke samu ba ya wuce shekaru 52 a duniya.
Mai rikon mukamin hukumar Alhaji Hassan Bashir ne ya bayyana hakan a yayin da yake gabatar da jawabi kan yawan al’ummar kasar nan, a babban taron na sashin majalisar dinkin duniya kan al’umma da bunkasa kasa karo na 52. Da ya mai da hankali kan tsayin rai a kashen duniya.
A cewar Alhaji Hassan Bashir hukumar lafiya ta duniya WHO na daukar tsayin rai na galiban kasashen duniya wajen duba irin cimakar da suke ci da kuma jariran da ake Haifa in har an cigaba da samun mace-macen jarirai a kasar nan.
Haka zalika mai rikon mukamin shugaban hukumar kidaya ta kasar nan ya ce kawo yanzu ana samun tsaka-tsakin yawan ‘yan Najeriya kasa da kaso 5 cikin 100 da suke da shekaru 60 a duniya a cikin yawan al’umma, yayin da gaba ki dayan tsayin ran ya karu zuwa fiye da kaso 55 na shekarun mutane.
Alhaji Hassan Bashir ya kuma ce a halin yanzu Najeriya na da yawan al’umma da ya kai miliyan dari da casa’in da takwas 198, bayan da ake samun karuwar yawan mutane a duk shekara yake kaiwa fiye da kaso cikin 100.