Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Najeriya kasa ta uku da ta fi kowacce kasa yawan mutane masu mutuwa a shekaru 50

Published

on

Hukumar kidaya ta majalisar dinkin duniya ta bayyana Najeriya a matsayin kasa ta uku a duniya da mafi yawa na al’ummar kasar basa haura shekaru hamsin da biyar a duniya suke mutuwa.

Rahoton hukumar wanda aka wallafa jiya Litinin ya bayyana cewa an samu dama-dama a shekarar 2019 na adadin al’ummar Najeriya da suke mutuwa ba tare da sun haura shekaru hamsin da biyar ba, idan akwa kwatanta da kasasken Sierra Leone da Chadi da kuma Jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

A cewar rahoton hukumar a kasashen Sierra Leone da Chadi da kuma Jamhuriyar Afirka ta tsakiya al’ummomin basa haura shekaru hamsin da uku zuwa da hudu suke mutuwa.

Sai dai rahoton ya kuma bayyana cewa kasashe irin su Afghanistan Somaliya da kuma Syria al’ummomin kan haura shekaru hamsin da tara zuwa sittin da biyar ko kuma saba’in da uku.

 

Kamar yadda rahotanni ya bayyana Najeriya na da kaso arba’in da hudu cikin dari na matsalar auren wuri da ake yiwa kananan yara, yayinda ake da kaso goma sha biyar zuwa sha tara na auren wadanda shekarun su suka kai mizanin da ake so.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!