Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

NPFL: Kano Pillars ta doke Abia Warriors

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars mai taken Sai masu gida tayi nasarar doke Abia Warriors da ci 2- 1 a wasan gasar Firimiya ta kasa NPFL.

An dai gudanar da wasan ne a filin Ahmadu Bello da ke Zaria a jihar Kaduna, wanda wasan shi ne mako na 14 a gasar.

Dan wasa Kalu Nweke ne ya fara zura kwallon farki a minti na 16, kana Sa’idu Musa ya warware kwallon da aka zura Pillars a minti na 27 bayan samun taimako daga Rabiu Ali Pele.

‘Yan wasan Kano Pillars

A minti na 56 ne dai dan wasa Abdullahi Musa ya tabbatar Pillars tayi nasara bayan zura kwallo da ya yi a wasan.

Wanda hakan ya sanya Kano Pillars ta samu maki uku a hannun tawagar Abia Warriors da ke jihar Abia a kudancin Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!