Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Rashin buga wasa a Kano ya jawo muna rasa kudi Miliyan 36-Kano Pillars

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars na rasa kusan Naira miliyan talatin da shida sakamakon rashin buga wasa a gida a kakar wasa ta shekarar 2020/2021.

Pillars wadda ta koma buga wasanta a garin Kaduna sakamakon bayyana rashin kyawun filin wasa na Sani Abacha da kamfanin da ke shirya gasar Firimiya na kasa LMC yayi.

Tawagar Kano Pillars ta buga wasa goma sha tara a kakar wasa da ta gabata a filin wasa na Ahmadu Bello dake Kaduna, kana sun fafata wasa bakwai a wasannin su na gida a wannan kakar a dai garin na Kaduna.

Inda suke rasa a kalla Naira miliyan goma sha uku a kudin tikiti da suke siyarwa a duk wasan da zasu kara a gida, wanda a kalla filin wasan ke daukar magoya baya a kalla dubu goma sha shida, kungiyar dai na karbar a kalla Naira dari biyu zuwa Naira Dubu daya ga duk wanda zai shiga kallon wasa.

Shugaban kungiyar Surajo Yahya Jambul ne dai ya bayanna hakan hakan a wata ganawa da manema labarai a makon da muke ciki.

Lamarin da ya sanya tuni shugaban kungiyar Jambul ya ce sun sanar da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje kan cewar suna son dawowa gida Kano, don ganin an baiwa magoya baya dama su dawo kallon wasan kungiyar, dan hakan zai karfafa gwiwar ‘yan wasan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!