Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

NPFL: Kwara United ta yi watsi da hukuncin kwamitin NFF

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kwara United ta yi watsi da hukuncin da kwamitin daukaka kara na hukumar kwallon kafa ta Najeriya ya yanke kan ranar wasa ta 34 a gasar cin kofin kwararru na kasa tsakanin Jigawa Golden Stars da Rivers United.

Kwara United dai ta kammala gasar ta bana da maki 65 da banbanci kwallaye 20, hakan ne ya ba su tabbacin zama na uku a teburin gasar tare da samun tikitin gasar cin kofin Afirka.

A hukuncin da kwamitin ya yanke na cire wa Jigawa Golden Stars maki uku da kwallaye uku ya kuma ba wa Rivers United, lamarin da ya sanya Kwara United ta dawo ta hudu a bisa teburin tare da rasa tikitin zuwa gasar cin kofin Afirkan.

Labarai Masu Alaka:

NPFL: Rivers United ta gabatar da korafi kan Jigawa Golden Stars

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta nuna rashin gamsuwar ta da hukuncin ta na kalubalantar shugabancin kwamitin.

Shugaban kungiyar ta Kwara United, Kumbi Titiloye ya ce shugaban kwamitin daukaka karar, Eddy Mark ma’aikacin gwamnatin jihar Rivers ne don haka akwai alamar tambaya kan hukunci da kwamitin ya yanke.

“Kwara United ta yi watsi da wannan hukunci kuma za ta sanar da NFF kafin ta daukaka kara zuwa Kotun hukunta laifukan wasanni,” in ji Titiloye.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!