Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

NPFL: Sunshine Stars ta nada sabon mai horaswa

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Sunshine Stars ta nada Gbenga Ogunbote a matsayin sabon mai horas da kungiyar.

Ogunbote zai yi aiki da kungiyar a karo na biyu, bayan da ya jagoranci dayan tsagin kungiyar dake a garin Akure a shekarar 2012 zuwa ga kaiwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin kwararru na kasa.

Hukumar kula da kwallon kafa ta jihar Ondo wadda kuma ke jagorantar harkokin wasannin kungiyar ta Sunshine ce ta sanar da nada mai horas wa Ogunbote a garin Akure dake jihar ta Ondo.

Shugaban hukumar ta jihar Tajudeen Akinyemi, ya ce, “An zabi Ogunbote ne a matsayin mai horas da kungiyar duba da kwarewarsa da kuma sanin makamar aikin horas wa a kasar nan.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!