Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Wolverhampton: Ta dauki Nelson Semedo daga Barcelona

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Wolverhampton Wanderers ta dauki dan wasa Nelson Semedo daga Barcelona a kan kudi Euro miliyan 37.

Mai horas da kungiyar Nuno Espirito Santo, ya ce, dama ya na neman dan wasan da zai maye gurbin Matt Doherty wanda ya koma kungiyar Tottenham Hotspur a watan da ya gabata.

“Kowa ya sani wannan ba karamar nasara ba ce, dauko kwararren dan wasa daga fitacciyar kungiya a fadin duniya,” shugaban kungiyar ta Wolves Jeff Shi.

Nelson Semedo dan kasar Portugal mai shekaru 26, ya taka wa Barcelona wasanni 124 a yayin da ya buga wa Portugal wasanni 13.

Semedo dai ya zama na uku a cikin ‘yan wasan da Wolves ta saya yayin da aka fara cinikayyar ‘yan wasa a bana, bayan zuwan Fabio Silva daga FC Porto sai kuma Ki-Jana Hoever daga Liverpool.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!