Kiwon Lafiya
NPHCDA:Rashin yin riga-kafi ne ya jawo barkewa cutar mashako
Gwamnatin Nigeria ta hannun hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasa NPHCDA ta ce barkewar cutar Mashako a jihar Kano da sauran jihohin kasar wata alama ce da take nuna rashin karbar rigakafin da akeyiwa yara tun daga randa aka haife su zuwa shekara daya yadda ya kamata.
Babban daraktan hukumar Dakta Faisal Shuaib ne ya bayyana hakan jiya Asabar a Abuja, yayin da yake magana kan bullar cutar da aka samu a jihar Kano da wasu jihohi.
Dakta Faisal Shuaib, ya ce ‘cutar diphtheria cuta ce da za a iya rigakafinta, tare da cewa kiyaye alluran rigakafin shi ne kadai hanyar kariya daga kamuwa da cutar.
Wanda yayi kira ga iyaye da masu kula da yara a jihar Kano da sauran sassan Nijeriya da su tabbatar an yiwa ‘ya’yansu ‘yan kasa da shekara Daya cikakken allurar rigakafin da suke bukata.
Ya Kuma ce ‘hukumar ta hada kai da jihar Kano da kananan hukumomin da abin ya shafa, da kuma masu Kula da bangaren rigakafi domin inganta ayyukan rigakafin a jihar.
You must be logged in to post a comment Login