Labarai
Nuhu Ribadu ya jagoranci tawaga ta musamman zuwa Amurka don tattaunawa

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jagoranci wata tawaga ta musamman zuwa ƙasar Amurka domin tattaunawa kan zargin da wani ɗan majalisar wakilai na Amurka ke yi cewa, ana cin zarafin Kiristoci a Najeriya.
A cewar majalisar tsaron Najeriya wannan zargin na iya haifar da matsalolin fahimta tsakanin al’ummomi tare da bata sunan Najeriya a idon duniya, saboda haka gwamnatin tarayya ta ga dacewar tura tawaga ta musamman don gabatar da hujjoji da bayanai na gaskiya.
Tawagar ta yi bayanin cewa Najeriya ƙasa ce mai al’adu da addinai daban-daban wadda ke kare hakkin kowane ɗan ƙasa ba tare da nuna wariya ba.
You must be logged in to post a comment Login