Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NUJ Freedom Radio ta taya Wasila Ibrahim Ladan murnar samun nasara

Published

on

Kungiyar ‘yan Jaridu ta kasa reshen tashar  Freedom Radio Kano, ta taya kwamrade Wasila Ibrahim Ladan murna, a matsayin sabuwar sakatariya ta Kungiyar ‘yan Jaridu mata ta kasa NAWOJ.

Wannan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabar kungiyar kwamrade Aisha Muhammad Yalleman da Sakataren kungiyar Kwamrade Muzamil Ibrahim Yakasai.

Ta cikin sanarwa, Kwamrade Aisha ta ce, Kwamrade Ladan ta cancanci matsayin da ta samu na sakatariya, sakamakon kwazonta da hangen nisanta akan ‘yan Jaridu mata a fadin Najeriya.

Sanarwa ta kuma ta ya Hajiya Aisha Ibrahim Bura murna a matsayin sabuwar shugabar kungiyar NAWOJ.

Kwamrade Aisha Yalleman ta yi fatan Hajiya Bura za ta hada kan ‘yan jarida mata na kasar nan, da nufin ciyar da kungiyar gaba, tare da fatan cewa, kungiyar za ta ci gaba da bai wa ‘yan jaridun horo akai akai ganin yadda aikin jarida a yanzu ke tafiya da zamani.

An dai gudanar da zaben kungiyar ta NAWOJ a ranar Asabar, Ashirin da biyar ga watan Nuwanban nan da muke ciki, a birnin tarraya Abuja.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!