Labarai
NYSC: Ta hana dalibai zuwa aikin hidimar kasa a makarantu 8
Hukumar kula da matasa ‘yan hidimar kasa ta fitar da sunayen wasu makarantu guda 8 daga kasashen waje guda uku da ba ta amince su yi aikin hidimar kasa ba.
Kasashen sun hada da Jamhuriyar Benin da Nijar da kuma Cameroon.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta umarci jami’anta na Jihohin kasar nan da kuma birnin tarayya Abuja da su yi aiki da ita a lokacin da suke tantance matasa ‘yan hidimar kasa na bana.
Makarantun sun hada Al-Nahda International University da ke Jamhuriyar Nijar, da International University Bamenda ta kasar Cameroon, sai kuma guda 6 daga Jamhuriyar Benin da suka hada da Ecole Superieur Sainte Felicite.
Da Ecole Superieur D Adminstartion et DEconomie, da Ecole Superieur DEnseignement Professionelle Le Berger, da Ecole Superieur St. Louis D. Afrique.
Sai Institute Superieur de Comm. Dord Et de Management, da kuma Institut Superieur de Formation Professionelle.
You must be logged in to post a comment Login