Labarai
Rundunar sojin ruwa ta Najeriya ta sauyawa jami’ai 257 wuraren aiki
Rundunar sojin ruwan kasar nan ta sauyawa jami’anta 257 wuraren aiki da suka hadar da Rear Admiral guda 60 da Commodore 123 da kuma Kyaftin 74.
Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran rundunar Sulaiman Dahun ya fitar.
Sanarwar ta ce, sauyin wuraren aikin ya samu amincewar babban hafsan sojin ruwa na Najeriya Vice Admiral Auwal Zubairu Gambo.
Haka zalika sanarwar ta kara da cewa matakin ya zo ne sakamakon sauyin manyan hafsoshin tsaron kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login