Labarai
NYSC ta sanya ranar yaye ‘yan hidimar kasa rukuni na biyu
Hukumar kula da matasa ‘yan hidimar kasa ta sanar da cewa a ranar 16 ga watan Yulin nan da mu ke ciki ne za ta yaye matasa ‘yan hidimar kasa ‘yan rukuni na biyu.
Wannan na cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar yau mai dauke da sa hannun daraktar yada labaranta Mrs Adenike Adeyemi, tana mai cewar za a gudanar da bikin yaye matasan ne bisa matakan kariya daga yaduwar cutar Covid-19.
Sanarwar ta kara da cewa matasan za su karbi shaidar kammala hidimar a kananan hukumomi a cikin kwanaki goma, don tabbatar da bin matakan da cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta gindaya na hana cunkoso.
Ta cikin sanarwar, shugaban hukumar Birgediya Janar Shu’aibu Ibrahim ya taya matasan murnar kammala hidimar, sannan ya ja hankalinsu da su ci gaba da kasancewa ‘yan kasa nagari a duk inda suka samu kansu.
You must be logged in to post a comment Login