Labarai
Ofishin Akanta na Najeriya ya kalu balancida maganar wasu jaridu
Ofishin akanta Janar na Najeriya ya musanta rahotannin da wasu jaridun kasar suka yada cewa Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu, ya ce, tattalin arzikin Najeriya na daf da shiga halin tagayyara.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai Magana da yawun ofishin akanta Janar na kasa, Henshaw Ogubike.
Sanarwar ta ce, jaridar ‘The Nation’ da wasu jaridu da ake wallafa su a kafofin sada zumunta, sun ruwaito cewa, Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu, ya yi ikirarin cewa, tattalin arzikin Najeriya na daf da tagayyara sakamakon manufofin tattalin arziki maras inganci.
A cewar jaridun, Sarkin na Kano ya kalubalanci ci gaba da tsarin biyan kudin tallafin mai da kuma na lantarki.
Sanarwar ta musanta kalaman tana mai cewa, babu kanshin gaskiya game da rahotanni da jaridun suka yada, domin kuwa Sarki shawara ya bai wa gwamnati kan cewa, ta dauki gabarin janye tallafin mai dana lantarki saisa-saisa wanda hakan zai taimakawa gwamnati wajen samun isassun kudade da za su gudanar da ayyukan raya kasa.