Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tattalin arzikin Najeriya na gab da durkushewa -Muhammadu Sanusi Na II

Published

on

Tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN), Malam Muhammadu Sanusi, na II, ya ce tattalin arzikin Najeriya na gab da durkushewa.

Muhammadu Sunusi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen rufe babban taron zuba jari na jihar Kaduna a ranar Juma’a 24 ga watan Satumbar shekarar 2021.

Kotu ta saka ranar da za ta kawo karshen shari’ar tsohon sarki Muhammadu Sunusi na biyu da gwamnatin Kano

Tsohon gwamnann bankin kuma tsohon sarkin Kano ya ce kasar nan na fama da kalubale  wajen hakar man fetur, a cewar sa ya zama wajibi a mayar da hankali wajen inganta tattalin arzikin kasar.

Ya kuma ce nan bada dadewa ba za’a iya rasa sinadarin dake bayar da Zinare a kasar nan, idan har ba’a mayar da hankali wajen inganta bangaren ba.

Muhammadu Sanusi ya ce, yayin da kasar Ghana dake da karancin tattalin arzikin kasa, ke saka kudade masu yawa a bangaren ilimi, ita kuwa Najeriya na saka kashi 7 cikin 100 kawai a bangaren.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!