Labaran Wasanni
Okoye da Iwobi na ci gaba da karbar sakawannin barazana ga ƴan Najeriya
Mai tsaran gida na kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Maduka Okoye da kuma dan wasan tsakiya Alex Iwobi, suna ci gaba da karbar sakwannin barazana daga wajen magoya bayan kungiyar.
Wannan dai na zuwa ne bayan da kungiyar ta fice daga gasar cin kofin Africa Cup of Nations da ake gudanarwa a kasar Kamaru sakamakon rashin nasara da ci 1-0 da nema a hannun kasar Tunisia a ranar Lahadi.
Dan wasa Youssef Msakni ne dai ya zura kwallayo daya tilo a ragar Super Eagles a yadi na 25 da hakan ya sa kungiyarsa kaiwa zagaye na kasashe takwas.
Wasu cikin magoya bayan tawagar na cewa kamata ya yi a ce mai tsaran gida Okoye ya hana shigar kwallon da Msakni’s ya zura, yayinda shi kuma Iwobi ake dora laifin jankatin da ya samu jim kadan bayan shigowarsa filin wasan.
A dai dai minti na 59 dan wasa Iwobi ya samu jankati bayan da ya yi sauyin dan wasa Kelechi Iheanacho.
Kawo yanzu dai ‘yan wasa
Okoye da kuma Iwobi suna ci gaba da fuskantar cin zarafi a shafikan sada zumunta daban-daban.
Lamarin da ya sanya dan wasan Everton goge shafinsa na Twitter da ya ke amfani da shi.
You must be logged in to post a comment Login