Labaran Wasanni
Old Trafford: Zai dauki ‘yan kallo 23,500 tare da bada tazara – Man United
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta canja tsarin filin wasanta na Old Trafford ta yadda zai dauke mutane 23,500 daidai da dokar bada tazara tsakanin ‘yan kallo.
A baya dai gwamnatin kasar ta Ingila ta amince da fara dawowa da ‘yan kallo da kadan-kadan a farko watan Oktoba kafin daga baya ta dakatar da yunkurin nata sakamakon cigaba da samun karuwar cutar Corona a kasar.
Jami’in kungiyar Collette Roche, ya ce “Mun karbi umarnin da ka’idojin da gwamnati ta gindaya kan batun dawowar ‘yan kallo filayen wasanni, kuma na tabbata sabon tsarin da muka yiwa Old Trafford zai bada kariya ga ‘yan kallo ta hanyar bada tazara”.
Man United na daya daga cikin kungiyoyin dake fuskantar matsalar kudaden shiga, yayin da tayi asarar sama da Yuro miliyan 70 tun a watan Yunin 2020 sakamakon annobar COVID-19.
A dai watan Satumba da ya gabata ne firayim minista Boris Johnson ya ce dokar hana ‘yan kallo shiga filayen wasa ka iya cigaba har tsawon watanni shida masu zuwa.
You must be logged in to post a comment Login