Connect with us

Labaran Wasanni

Za’a dawo gasar Bundesliga a watan Mayu

Published

on

Shugaban hukumar kwallon kafar jamus (DFL) Christian Seifert, yace ana shirye shiryen dawowa gasar a farkon watan Maris, ba ‘yan kallo.

A baya dai an dage gasar ta kasar Jamus, rukuni na farko dana biyu har zuwa ranar 30 ga watan Afrilun bana sakamakon barkewar cutar Corona Virus.

Rahotanni dai sun tabbar da cewa zuwa yanzu  kasar Jamus na daga cikin kasashen da suke kan gaba gaba wanda cutar tafi kamari a nahiyar Turai, da yawan mutane 110,000, da suka kamu da cutar in da zuwa  yanzu haka mutum 2,100 suka rasu.

Labarai masu alaka.

Muller ya saka hannu a sabon kwantiragi da Bayern Munich

Cutar Corona ta sa an dakatar da ‘yan kallo shiga wajen wasanni

Christian Seifert ya kara dacewa nan ba da dadewa ba za’a dawo gasar, wanda hakan zai kara karsashi ga al’umma da debe musu kewa a wannan hali da ake ciki, kuma a shirye suke da su taimakawa gwamnati a kokarin ta na yakar cutar da kuma jin shawarwarin ta kan yadda gasar zata kasance.

Siefert, ya kara dacewa kammala gasar akan lokaci zai kar bada wata dama ta sanin inda aka dosa a kwallon kafar nahiyar Turai ba ma kasar Jamus ba, in da yace sauke gasar gaba daya zai jefe kungiyoyi guda biyar daga gasar a cikin mummunan hali na rashin kudi, wanda hakan ka iya ja wo wa kungiyoyin rushewa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!