Kiwon Lafiya
Oluremi Tinubu:ta bukaci da gwamnatin tarraya ta bada hutun kasa don baiwa jama’a damar karbar katin zabe
‘Yar majalisar Dattijai mai wakiltar mazabar Lagos ta tsakiya Oluremi Tinubu ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ware ranaku domin bada hutu a fadin kasar nan don al’umma su samu damar karbar katinsu na zabe na dindindin.
Oluremi Tinubu na bayyana hakan ne a jiya Lahadi a Lagos, sakamakon gabatowar wa’adin watan Disamban bana don kammala karbar katin zaben.
Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ke cewa katunan zabe sama da miliyan bakwai ne a hannun hukumar, wanda kawo yanzu ba a karba ba.
‘Yar majalisar dattijan ta bukaci a fadada shirin rabon katin ya kai har lokacin hutun karshen mako don baiwa ma’aikata damar karbar na su katunan.
Sannan ta bukaci hukumar INEC da ta samar da duk wasu abubuwa da ake bukata domin saukaka aikin raba katin zaben na dinidindin