Labarai
Osinbajo zai bar Ajuja zuwa London

Mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo zai halarci wani taro a London.
Wannan na cikin sanarwar da Laolu Akande babban mataimaki na musamman ga Farfesa Yemi Osinbajo kan harkokin yaɗa labarai ya fitar.
Osinbajo zai bar Abuja a ranar Alhamis, domin wakiltar shugaba Muhammadu Buhari yayin babban taron da majalisar ɗinkin duniya za ta gudanar.
Taron za a gudanar da shi a ranar Juma’a a kwalejin Imperial da ke London.
You must be logged in to post a comment Login